#Taragon_A_A_Zaura_Media_Team.
A A ZAURA YA DAUKI NAUYIN AIKIN WATA YARINYA 🙏😢
A cikin kokarinsa na tallafawa Al-ummar Kano musamman akan harkar lafiya mai girma His Excellency Abdulsalam Abdulkarim A A Zaura ya dauki nauyin wata yarinya mai fama da ciwon Daji ( cancer ) a cinyarta a asibitin Mallam Aminu Kano yayin da yake da zagawa domin duba marasa lafiya tare da wani bawan Allah a satin daya gabata.
A A Zaura yayi alkawarin biyan dukkan kudaden da wadannan bayin Allah zasu bukata na maga
ni dakuma aikin da za a yi musu, haka kuma yayi kira ga yan kasuwa, ma'aikatan gwamnati, Malamai, sarakuna yan fansho, yan siyasa da masu hannu da shuni da su ringa tallafawa irin wadannan bayin Allah masu karamin karfi.
Daga karshe A A Zaura ya tallafawa majinyata da dama da kudaden siyan magunguna.
Muna addu'ar Allah ya saka masa da mafificin alkhairi ya biya bukatu amin summa amin.
Taragon A.A Zaura Media Team.
24/12/2023.
0 Comments