LABARI DA DUMI DUMINSA DAGA JIHAR KANO


Yanzu fisabillillahi, ya za'ai ace gwamnatin yan kungiya zasu gina gada akan kudi N15Billion, amma wai kashi 70% na kudin, da kudaden kananen hukumomi za'a biya? Wato kusan N10.5Billion kenan. Dan mey ya sa za'a ciri kudin


Tsanyawa ko Kiru ko Minjibir
a zo a gina gadar kasa a Gwale? Ita gwamnatin jiha mey ya sa baza su dauka a kudin su ba? 


Misali: naje garin Riruwai dake karamar hukumar Tudun Wada, kwata kwata hanyar bata da kyau. Mey ya sa gwamnatin jiha baza ta dauki kudin su ba na Local Govt ta gyara musu hanya? Kuma garin babu ruwa, shin wannan ba shi ya kamata ai musu amfani da kudin su a samar musu ba? 


Sannan gadar nan guda biyu ce, daya a Danagundi daya a Tal'udu, kuma kowacce N15Billion ce, kaga kenan kudin biyun sun kama N30Billion, ana maganar kenan idan duk a kudin local government zaa dauka, zaa kwashe musu sama da N20Billion. Wannan ba zalunci bane, daga gwamnatin da take ikirarin kwato wa talaka yancin sa? Ko talakawan cikin birni kawai suka damu da su banda na karkara?


Babban abin takaicin ma, shine umarnin da aka rubuta a takardar "pls treat as urgent" wato a fidda kudin cikin gaggawa. Kaga kenan sun san cewa basu da nasara a kotu, sun san cewa tafiya za suyi, kuma sun san cewa kotu ta rufe asusun gwamnatin jiha sai na kananen hukumomi, shine suke san amfanin da wannan damar su kwashe kudin Kano.


Wannan kadan ne daga cikin badakalar da gwamnatin yan kungiya ta ke tafkawa a jihar Kano. Allah kadai ya san mey Gawuna zai tarar idan ya hau kujerar nan in Sha Allah. Amma ina so na tabbatar musu cewa, duk abinda suka shuka sai sun girba. 


Salihu Tanko Yakasai 

Dawisun Kanawa 

Copied

Post a Comment

0 Comments