INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIM RAJIUN

 KOWA YA SHIRYA


Wannan yaron ya bata kwanaki a Zaria, yau an samu gawarsa a gona an kwakwule idon sa guda biyu


Daga cikin abinda na tsana a rayuwana shine cutar da kananan yara da kuma mata, har ga Allah wannan rayuwar ba zamu taba ganin daidai ba matukar ana aikata haka


Kullun ina fada, ka ji a ranka cewa kai kanka baka yadda da kanka ba balle wani, hakan zai taimaka maka sosai wajen tsallake makircin miyagun cikin mu


Jama'a mu cigaba da kiyayewa tare da tsananta addu'ah, iyaye su kasance masu sanya ido sosai akan 'ya'yan su 


Mu yi kokarin koya wa 'ya'yan mu addu'ah na neman tsarin Allah wanda suka tabbata daga Annabi (SAW), shine babban makamin da zamu bawa kawunan mu da 'ya'yan mu domin ta zama garkuwa daga fadawa tarkon macuta da matsafa


Addu'ah ce kadan za'ayi sai tayi tasiri, amma duk mun watsar, shiyasa makiya suke samun nasara akan mu


Muna rokon Allah wadanda suka kashe yaron nan Allah Ya hadasu da mafi munin cutar damuwa da firgici a duk inda suke


Allah Ka jikan yaron, Ka sa mai ceton iyayensa ne 😭


Post a Comment

0 Comments