Da Dumi Duminsa!!!
Daidai lokacin da mafi yawa daga al'ummar jihar Kano ke murnar saura kiris gwamnati mai ci a yanzu a jihar ta gusa ta bayar da waje ga gwamnatin Nasuru Yusuf Gawuna da Murtala Sule Garo, bisa Yardar Allah, wasu kuma jininsu ne ke kara hawa hankalinsu na kara gushewa.
Musamman da a ka ce Supreme Court, ta bayar da cewa ranar Alhamis din nan mai zuwa za a yi zama daya tilo na sauraran duk bangarorin guda biyu. Kafin kuma a sa ranar yanke hukunci. Wanda mu na daf da ranar. Ranar ta na kusa kusa fa sosai. Wanda ya sani ya sani.
Wani bayanin karkashin kasa da muke samu ya nuna cewar dukkan jagororin gwamnatin rikon kwarya ta Kano jiya jiyan nan su ka gama gayawa kan su gaskiya cewar tafiya fa ta zo karshe. Sannan kuma sun amince da cewar wadanda za su iya gayawa magoya bayansu to a fara gaya musu gaskiya tun yanzu.
A dalilin hakan an ce da yawa daga cikin wadannan jagororin sun fara barin jihar sun ce ba za ma su iya zama a garin ba, balle ma su kara haduwa da wani bakin cikin da za su kara shiga bayan zaman Alhamis na sauraren bangarori da Supreme Court za ta yi.
Yayin da kuma a daya hannun jagororin bangaren jam'iyyar APC ke kara kwararowa gida Kano domin shirye shiryen karbar mulki. A halin da a ke ciki ma yanzu haka an ce akwai wasu daga 'ya' yan gwamnatin rikon kwarya da su ka fara wani mitin na sirri dan sanin ta bangaren wane jigo daga cikin jigogin APC ya kamata su dawo wajen Baba Ganduje bayan Supreme Court ta gama tarwatsa gwamnatin ta su.
Sannan labari ya tabbata cewar akwai jiga jigan jam'iyyar APC na kasa wadanda da su za a yi bikin rantsuwar a Kano. Wani babban labarin farin cikin ma ba zai fadu a social media ba. Amma dai ba abinda za mu ce sai dai Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah.
Kano sabuwa nan da 'yan kwanaki kadan masu zuwa. Ba dan gudun kar wasu su kasa cin abinci ba ma, da mun fadi takamaimai ranar. Kuma mu na gudun bai kamata a ce an ji ranar daga wata majiya ba sabanin Supreme Court.
ALKALAN SUPREME COURT ALLAH NE KADAI ZAI IYA BIYANKU SABODA ADALCIN DA KU KA SA A GABA.
0 Comments