EFCC Za Ta Yiwa Sadiya Farouk Tambayoyi Kan Badakalar N37bn
Ana binciken ta ne kan zunzurutun kudi har Naira biliyan 37.1 da ake zargin an wawure a karkashin kulawarta ta hannun wani dan kwangila, James Okwete.
Ana sa ran Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) za ta yi wa tsohuwar ministar harkokin jin kai, magance bala’o’i da ci gaban jama’a, Sadiya Umar-Farouk tambayoyi kan badakalar Naira biliyan 37.1.
Wata majiya mai karfi ta EFCC ta tabbatar da hakan ga gidan talabijin na Channels a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Laraba.
Sadiya Umar-Farouk ta rike mukamin minista a lokacin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari daga watan Agustan 2019 zuwa ranar 29 ga Mayu, 2023.
A makon da ya gabata ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gayyaci tsohuwar ministar bayan wani bincike da aka gudanar kan ayyukanta a ma’aikatar a lokacin da ta rike madafun iko.
Ana binciken ta ne kan zunzurutun kudi har Naira biliyan 37.1 da ake zargin an wawure a karkashin kulawarta ta hannun wani dan kwangila, James Okwete.
Bayan mako guda, an bukaci tsohuwar ministar ta bayyana a gaban masu bincike a hedikwatar EFCC da ke Jabi, Abuja, da karfe 10:00 na safe.
Sai dai har yanzu ba ta bayyana a hedikwatar EFCC ba, inji majiyar da ta nemi a sakaya sunanta.
A cewar majiyar, an kuma gayyaci wasu jami’an da suka yi aiki da ita domin su ba da haske kan yadda al’amuran ma’aikatar suka kasance cikin shekaru hudu da suka gabata.
An dakatar da shugaban NSIPA
Tambayoyin da aka shirya yi wa tsohuwar ministar ya biyo bayan dakatarwar da shugaba Bola Tinubu ya yi wa Halima Shehu a matsayin babbar jami’a (Shugaba) da kuma kodineta a hukumar kula da harkokin zuba jari ta kasa (NSIPA).
Tinubu ya maye gurbin Halima da Manajan shirye-shiryen N-Power na kasa, Akindele Egbuwalo, a matsayin mukaddashinsa har sai an fara bincike kan ayyukan tsohuwar shugabar hukumar.
NSIPA, wacce ke da alhakin gudanar da muhimman shirye-shirye kamar N-Power da Canjin Kudi na Sharadi, an yi ta bincike a 'yan kwanakin nan.
Hukumar tana karkashin ma’aikatar kula da jin kai.
Sai dai ba a san dalilin da ya sa aka dakatar da Shehu ba, an tattaro cewa shugabar NSIPA da ke fama da rikici ita ma tana da tambayoyi da zata amsa.
.
0 Comments