LABARAI

 Abdussamad Bua Ya Sami Ribar Naira Tiliyan 2.3 Daga Kamfanoninsa Biyu A Shekara Daya..


Hamshakin attajirin nan na Najeriya, Abdul Samad Rabi’u ya sami gagarumar riba daga kamfanonin sa guda biyu na BUA Cement da BUA Foods, sun samar masa da ribar naira tiriliyan 2.3 a shekarar 2023.


Wannan shine mafi girman ribar babban jari na kowane hamshakin attajirin da ke da sha'awar sarrafa kamfanoni da aka jera akan NGX.


Ribar da aka samu na nuna karuwar kashi 194 cikin 100 a kowace shekara ta fuskar kimar kasuwa ga masu hannun jarin kamfanin, musamman Abdussamad Rabiu wanda ke kula da mafi yawan hannayen jarin kamfanonin.


A baya dai kididdigar ta bayar da rahoton cewa an rage dukiyar attajirin da dala biliyan 2.5 a shekarar 2023, sakamakon faduwar darajar Naira.


Duk da haka, bisa la'akari da babban jari, dukiyarsa ta zuba jari a waɗannan kamfanoni fiye da ninki biyu.


.


Post a Comment

0 Comments