WATA SABUWA A NIGERIA


 Wata Sabuwa: Naira 1,200 Yakamata A Siyar Da Litar Man Fetur - 'Yan Kasuwar Mai..


Kamfanin NNPCPL da ‘yan kasuwar mai sun yi jayayya kan tallafin mai, dillalan man fetur din sun dage kan Naira 1,200/lita


A ranar Talatar da ta gabata ne Kamfanin Mai na Najeriya da masu sayar da mai a karkashin kungiyar masu sayar da man fetur ta Najeriya, suka sake yin artabu kan cire tallafin man fetur.


Hakan dai ya zo ne a daidai lokacin da faduwar darajar Naira akan dalar Amurka a duka kasuwar masu saka hannun jari da masu fitar da kayayyaki da kuma kasuwannin bayan fage.


A ranar Talata, an canjin kuɗin gida a kan 998 / dala a kasuwar hukuma, yayin da ake ciniki a kan 1,225 / dala a kasuwar baƙar fata.


Dangane da faduwar darajar Naira, masana tattalin arziki da masu sayar da man fetur sun ce tallafin PMS na karuwa a ‘yan kwanakin nan, sai dai hukumar NNPC ta yi gaggawar dakile wadannan matakai tare da bayyana cewa ta na dawo da kudaden da ta kashe wajen shigo man fetur.


Babban jami’in gudanarwa na Kamfanin Samar da Kudi, Bismarck Rewane, ya yin wani shirin kai tsaye a gidan talabijin na ChannelsTV a ranar Lahadin da ta gabata, ya bayyana cewa ba a cire tallafin man fetur ba amma an rage shi.


Hakazalika, ‘yan kasuwar man sun shaida wa wakilinmu a ranar Talata cewa, tallafin man fetur yana karuwa idan aka yi la’akari da faduwar da Naira ta yi kan dalar Amurka da kuma tsadar danyen mai, inda suka jaddada cewa PMS ya kamata a sayar da shi kan Naira 1,200/lita.


Man Fetur, NNPCL ne kadai ke shigo da shi Najeriya, a halin yanzu ana sayar da shi tsakanin N617/litta zuwa Naira 660, ya danganta da inda ake siya a Najeriya.


Shima da yake nasa jawabin, babban jami’in cibiyar bunkasa sana’o’in hannu, Dakta Muda Yusuf, ya ce akwai wani bangare na tallafin man fetur, amma ya lura cewa gwamnati ce ke ba da tallafin saboda siyasa, zamantakewa da tattalin arziki.


✍️ 

Post a Comment

0 Comments