LABARAI DAGA KADUNA

 Da dumi'dumi: Gwamna Uba sani ya kaddamar da Kwamitin da za'a sake Gina Garin Tudun Biri wanda sojojin Nageriya suka kashe 'yan Maulidi bisa kuskure.


Gwamnan Jihar Kaduna Mal Uba Sani ya kafa wani kwamiti na musamman domn gudanar da sake Gina kauyen Tudun Biri wanda sojojin suka kashe Yan Maulid sama da mutun 120 a bisa kuskure Gwamnatin Tarayya, Majalisar Dokoki ta Kasa, Kungiyar Gwamnonin Nijeriya, kamfanoni, da ‘yan Najeriya masu kishin kasa duk sun bayar gudunmuwarsu domun tallafawa Al’ummar ta Tudun Biri Dake Karamar Hukumar Igabi a jihar.


Mataimakiyar Gwamna Dr Hadiza Sabuwa Balarabe ce za ta jagoranci kwamitin, yayin da mambobin kwamitin za su fito ne daga wakilan wadanda rikicin Tudun Biri ya rutsa da su da shugabannin al’ummar  Tudun Biri da na Karamar Hukumar Igabi, da kuma Gwamnatin Jihar Kaduna.





Post a Comment

0 Comments